HomeLabaraiZan rage haraji in hako danyan man Borno - Atiku

Zan rage haraji in hako danyan man Borno – Atiku

Date:

Related stories

INEC ta ce ba a kammala zabe a jihar Adamawa ba

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ayyana zaben gwamnan jihar...

An kashe ‘yan sanda 2, da dama sun raunata a wata arangama da sojoji a Taraba

A ranar Litin ne wasu sojoji suka kashe ‘yansanda...

Gwamna Zulum ya sake lashe zaben gwamna a jihar Borno

Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar...

Sojoji sun kashe hatsabinin dan ta’adda Umaru Nagona

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka, Umaru Nagona, daya daga...

An kona gidan mawakin siyasa Rarara a Kano

Wasu da ake zargi ’yan daba ne sun banka...

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi alkawarin rage haraji da kuma hako danyen mai da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da Tafkin Chadi idan ya ci zabe.

Dan takarar, yayin kaddamar da yakin neman zabensa na yankin Arewa maso Gabas, a Maiduguri, Jihar Borno, ya yi alkawarin farfado da Tafkin Chadi, bukatar da ya ce, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai, ya yi.

A jawabinsa ranar Laraba a Maidugri wadda ita ce cibiyar kungiyar Boko Haram, dan takarar ya yi alkawrin magance matsalar tsaron da ta addabi yankin da ma sauran yankunan Najeriya.“Kafin zuwata nan na ziyarci Fadar Shehun Borno, kuma a jawabinsa ya bukaci mu magance wasu matsaloli hudu ko biyar da ke addabar Borno.“Na farki shi ne dawo da tsaro da zaman lafiya a jihar kuma na yi masa alkawari cewa za mu yi, idan Allah Ya kai mu PDP ta ci zabe za a samu tsaro da aminci a Borno.

“Na biyu shi ne mu farfado da Tafkin Chadi domin manoma su koma gonakinsu su ci gaba da samar da abinci da ayyukan yi.

“Ya bukaci mu tabbata kananan hukumomi sun samu wutar lantarki, muka yi alkawarin yi.

“Haka kuma ya bukaci mu dawo da hakar danyen mai a yankin Tafkin Chadi, shi ma mun yi masa alakwarin da yardar Allah.”

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories