Jami’an tsaro sun kashe kasurgumin dan bindigar nan, Dogo maikasuwa a Kaduna

0
74

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kashe wani kwamandan ‘yan bindiga da aka fi sani da Dogo Maikasuwa a wani kazamin artabu da jami’an tsaro suka yi.

A wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce Dogo Maikasuwa wanda aka fi sani da ‘Dogo Maimillion’ ya jagoranci hare-hare da sace-sacen jama’a da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia da kuma kananan hukumomin Chikun da Kajuru a jihar.

Sanarwar ta bayyana Dogo a matsayin daya daga cikin ‘yan ta’adda mafi gawurta da ke jagorantar sauran al’umma wajen ta’addanci a jihar.

Aruwan ya kara da cewa, Dogo ya jagoranci ‘yan bindiga nasa wajen aikata ta’asa da muguwar dabi’a, inda sukan kashe wadanda aka yi garkuwa da su a lokacin da aka jinkirta kai musu kudin fansa.

Aruwan, ya ce sauran ‘yan bindigar sun tsere da raunukan bindiga.