Buhari ya sauka a Abuja bayan duba lafiyarsa a Landan

0
48

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo bayan bulaguron da ya yi domin duba lafiyarsa a Birtaniya.

A wani saƙo da mataimakin shugaba na musamman kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi da maraice ya ce shugaban ya sauka a Abuja babban birnin ƙasar.

Shugaban ya kwashe kusan makonni biyu a birnin Landan, bayan da ya bar ƙasar ranar 31 ga watan Oktoba domin a duba lafiyarsa.

A lokacin bulaguron nasa Shugaban Buhari ya ziyarci sarki Charles lll a fadarsa da ke Buckingham.