Jam’iyyar PRP ta kaddamar da kwamitin yakin zaben shugaban kasa

0
119

Kamar sauran jam’iyyun siyasa a Najeriya, itama jam’iyyar PRP, ta kaddamar da kwamitin yakin zaben shugaban kasa a zaben da za a yi a 2023.

A ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba ne jam’iyyar PRP,ta kaddamar da kwamitin.

A yayin kaddamar da kwamitin, PRP ta bayyana kudurorinta ga al’ummar kasarnan da zata yi amfani da su wajen kawo sauyi ga rayuwar ‘yan kasar idan ta samu nasara a zaben.

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PRP, Kola Abiola, ya bayyana manufofin jam’iyyar a wajen taron, in da ya fara da batun bunkasa tattalin arzikin kasa.

Mr Kola Abiola, ya ce,” Bunkasa noma da kiwo na daga cikin manufofin jam’iyyar mu, da ilimi da tsaro dama bunkasa ma’adinun kasa.“

Dantakarar na PRP, ya ce tuni suka yi tsare-tsare kan yadda zasu gudanar da ayyukansu idan har suka samu nasara.

Daya daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar ta PRP, farfesa Attahiru Jega, ya shaida wa BBC cewa, amincewa da akidar PRP, ne ya sa ya zama mamba a cikinta.

Ya ce, suna da mutane jajirtattau a cikin jam’iyyarsu, sannan akai matasa masu ilimi da kishin kasa a cikinta.

Farfesa Jega, ya ce ‚‘‘ Tuni muka dukufa muna ta fadarkar da jama’a a kan sanin cewa bisa la’akari da yadda kasar ke ciki, dole a samu mutanen da zasu sadaukar da kansu su kawo gyaran da zai amfai jama’a da ma kasa baki daya.“

Farfesan, ya ce sun kuma ja hankalin mutane a kan su fahimci cewa karbar kudi don a sayi kuri’ar mutum ba zai taba kawo ci gaba a kasar ba.

Tuni dai sauran jam’iyyun kasar kamar APC da PDP da NNPP, a Najeriyar suka kaddamar da nasu kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar jam’iyyunsu, inda tuni suka fara yakin neman zaben.