NPC ta sha alwashin gudanar da sahihiyar kidaya a 2023

0
52

Hukumar kidaya ta kasa NPC ta sha alwashin gudanar da sahihiyar kidayar mutane da gidaje a fadin Nijeriya a 2023.

Kwamishinan hukumar NPC a Jihar Katsina, Injiniya Bala Almu Banye ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai dangane da bude shafin yanar gizo na daukar ma’aikatan da za su gudanar da aikin kidayar.

Ya yi nuni da cewa bin hanyar zamani wajen daukar ma’aikatan kidayar wani bangare ne na kudurin hukumar na gudanar da sahihi kuma ingantacciyar kidaya.

Injiniya Almu ya kara da cewa yawan ma’aikatan kidayar da za a dauka ya danganta da yawan yankuna da ke fadin kasar nan.

Ya ce hukumar ta kafa tawagar daukar ma’aikatan kidayar na kananan hukumomi da na jiha domin tabbatar da ganin an dauko mutanen da ke yankunan don gudanar da aikin.