Kwanaki shida gabanin fara gasar lashe kofin duniya a Qatar, a karon farko kasar ta sanar da kama mutane uku da ke saida tikitin kallon gasar na bogi, a wasu haramtattun wurare sabanin wadanda gwamnati ta tanada a birnin Doha.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fidda wata sanarwa a shafinta na Twitter da ke cewar, dukkanin mutane ukun da aka kama ba ‘yan kasar ba ne, amma sai dai ba ta bayyana kasashensu na asali ba.
Sanarwar ta ce, idan aka tabbatar da laifin wadanda ake zargin, za a ci su tarar Riyal dubu dari 250 kwatan-kwacin Dala dubu 68 kowannensu.
Mutane dai na cincirindo a halastattun cibiyoyin sayar da tikitin kallon gasar a birnin Doha, lamarin da ya haifar da dogayen layuka.
Ko a farkon watan nan dai, sai da aka kama wasu da ke sayar da kofin gasar na bodi ta bayan fage sabanin wuraren da aka tanada don yin hakan.