Boko haram ta yi wa mata yankan rago saboda zargin maita

0
120
Mayakan Boko Haram sun kashe wasu mata a Jihar Borno bayan sun zarge su da maita wanda a cewarsu sun lashe kurwar wasu ’ya’yan daya daga cikin kwamandojin mayakan.

A makon jiya ne, Boko Haram ta tsare mata 40 a kusa da kauyen Gwoza bayan kwamandan mayakan, Ali Guyile ya ba da umarnin haka.

Wannan dai ya faru ne jim kadan da mutuwar ‘ya’yansa da ya ce, mayun ne suka lashe kurwarsu kamar yadda wata mata da ta tsira ta shaida wa manema labarai.

Kwamandan na Boko Haram mai shekaru 35, ya bai wa mayakansa umarnin gadin duk wani gida da ake zargin akwai mayya a cikinsa, kafin daga bisani ya yi wa wasu daga cikinsu kisan gilla ta hanyar yankar rago.

Matar da ta tsira ta shaida wa Gidan Rediyon Faransa cewa, tuni ta nemi mafaka a birnin Maiduguri bayan ta kubuta daga hannun mayakan kuma a cewarta, mata 14 ne suka kashe a ranar Alhamis da ta gabata bisa zargin su da maitar.

Sannan kwamandan ya ce, zai ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo karin matan da ke da hannu a mutuwar ‘ya’yan nasa kamar yadda matar da shaida.

Gwamnatin Jihar Borno ta ce, tana gudanar da bincike a bangarenta game da wannan al’amari.