Nabeela Syed, mace Musulma ta farko da aka zaba a majalisar dokoki ta Amurka

0
62

Nabeela Syed, ‘yar asalin kasar Indiya mai shekaru 23, ta kasance mace musulma ta farko da aka zaba a matsayin ‘yar majalissar jihar Illinois dake kasar Amurka.

Ba’amurkiya musulma ‘yar asalin kasar Indiya, Nabeela Syed a ranar Laraba ta samu farin ciki sosai bayan da ta lashe zaben tsakiya na Amurka a majalisar dokokin jihar Illinois, inda ta doke dan takarar jam’iyyar Republican Chris Bos.

Nabeela ta bayyana hakan ne a shafinta na sada zumunta, nan take labaran suka fara karade lunguna da sako na duniya. “Sunana Nabeela Syed. ‘Yar shekara 23 Musulma ce, mace Ba-Amurkiya.

“Mun samu nasarar kwace gujera a gundumar mu da ke karkashin jam’iyyar Republican,” kamar yadda ta rubuta a shafin ta na Twitter.