Indiya ta yanke shawarar rage kudin aikin hajjin 2023 da akalla Rufi dubu100.
Minista Smriti Irani, ne ya sanar da hakan a taron Hajjin Indiya da aka yi a New Delhi a ranar Asabar, 12 ga Nuwamba, 2022.
Taron ya samu halartar mambobin Babban Kwamitin Hajji, tare da shugabannin kwamitocin alhazai na jihohi.
Hakan ya biyo bayan wani gagarumin zargi na cewa an kara kudin tafiyar Hajji daga Indiya a bara.
Tafiya zuwa Makkah ta karkashin Kwamitin Hajji na Indiya ta fi sauki a kan tafiya ta kamfanonin sufuri masu zaman kansu.