Abin da ya sa Arewacin Najeriya ya fi kudu talauci – Masana

0
70

‘Yan Najeriya ciki har da masana tattalin arziƙi na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan rahoton da Hukumar Ƙididdiga ta fitar, da ke nuna cewa mutum miliyan 133 ko kuma kashi 63 cikin 100 na ‘yan ƙasar ne ke fama da talauci.

Rahoton ya ce kashi 65 cikin 100 na matalautan Najeriya wato mutum miliyan 86, suna zaune ne a arewa.

Rahoton ya  bayyana Ondo a matsayin jihar da ta fi ƙarancin matalauta da kashi 27 cikin 100,

Yayin da Sakkwato ta fi yawan matalauta inda kashi 91 na ‘yan jihar ke fama da talauci.

Masana dai na cewa akwai tazara mai karfi tsakanin masu arziki da talaka, duk da cewa kasar mai arziki ce talakawanta sun fi yawa.

Sai dai ko mene ne dalilin da ya sa talauci ke karuwa a arewa?

Talauci a arewcin Najeriya

Farfesa Kabiru Isa Dandago, masanin tattalin arziƙi a Jami’ar Bayero da ke Kano ya shaidawa BBC cewa Najeriya na cikin wani yanayi saboda kaso mai yawa na tattalin arzikin kasar na hannun mutane tsiraru.

Ya ce kididdiga da aka fitar a kan hanya take, saboda gwamnatocin da ake tayi a kasar tsawon shekara da shekaru sun gaza fito da hanyoyin tsuke tazara tsakanin masu hali da talakawa.

Rahotan ya nuna cewa mata da yara a arewacin Najeriya ne suka fi talauci, saboda rashin ba su damammaki na jari da kananan sana’o’i da ilimin da ya kamata, a cewar masani.

Ya ce a arewacin Najeriya ba a samun wadatuwar mutanen da ke shiga harkokin noma da kere-kere da fanin yawo ido da masana’antu.

Wadannan su ne dalilan da suka sa talauci da fatara da yunwa ke yawaita a arewa.