’Yan sanda sun kama mijin da ya azabtar da matarsa da yunwa

0
102

Rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe ta tabbatar da cafke wani magidanci bisa zarginsa da tsare matarsa na tsawon watanni yana azabtar da ita da yunwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Damaturu.

Ya ce kamen ya biyo bayan sammacin da wata Babbar Kotun Majistare da ke zamanta a garin Nguru ta bayar, inda ta bai wa jami’an ‘yan sanda reshen yankin damar cafke magidanci.

Abdulkarim ya bayyana cewar wanda ake zargin ya tsare matarsa ce a gidansa da ke Nguru, inda ya rika azabtar da ita da yunwa da kuma rashin ba ta kulawar da ta dace.

“Ba da jimawa ba za mu yi magana da wanda abin ya shafa wanda yanzu haka tana kwance a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Jihar Kano.

“Za a mika wanda ake zargin zuwa kotu kamar yadda aka nema,” in ji shi.

Aminiya ta rawaito yadda mahaifiyar mayar ta kubutar da ita daga dakin da mijin nata ya tsare ta.

Tun bayan fitar labarin lamarin, mutane da dama suka shiga kiraye-kiraye ga ‘yan sanda da gwamnatin jihar da su binciki lamarin.