A sakonsa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya ce maimakon azurta ’yan kasa gwamnati ta buge da jefa miliyan 133 daga cikinsu a kangin talauci.
A cewarsa, “Sun yi alkawarin raba mutum miliyan 100 da talauci, sai ga shi a hukumance sun jefa mutum 133 ciki.”
A baya, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana tsare-tsaren da gwamnatinsa ta shirya don cire ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci ya zuwa 2030.
A watan Satumba, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Kwadago da Raba Ayyuka, Kachollum Daju, ta fada wa manewa labarai cewa za a iya cimma wannan manufa muddin masu ruwa da tsaki suka yi aikinsu yadda ya kamata.
Sai dai kuma, a ranar Alhamis Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta ba da sanarwar ’yan Najeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci, wanda shi ne kwatankwacin kashi 63 na yawan al’ummar kasar.