Atiku baya jin kunyar caccakar Obasanjo a bainar jama’a – Tinubu

0
97

A ranar Asabar din da ta gabata ne dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, ya caccaki takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Tinubu ya bayyana Atiku a matsayin mutum marar kunya wanda ya yaki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a bainar jama’a.

Ya yi wannan jawabi ne a yayin taron yakin neman zaben shugaban kasa/Gwamnatin APC a garin Warri na jihar Delta.

Tinubu ya ce Atiku ya yi fada da tsohon ubangidansa kan yadda suka kashe kudi wajen yi wa budurwar su ayyuka.

Ya kuma bayyana cewa ba za a iya amincewa da jam’iyyar PDP ta shugabanci ba saboda rigingimun da ke cikin jam’iyyar.

“Kishiyoyinmu ba su da kunya, idan suna fada a fili; ta yaya za su yi tunanin mulki?

“Lokacin da Atiku yake can yana fada da ubangidansa a bainar jama’a. Suna ba mu labarin yadda suka kashe kudin PTF wajen siyan motoci ga ‘yan matan su a bainar jama’a; ba su da kunya.

“Ba su da kunya; za ku sake zabe su? ” ya tambaya.

Atiku ya taba zama mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Obasanjo.

A lokacin mulkin PDP na shekaru takwas, Atiku ya sha da kyar tsakaninsa da Obasanjo.