Benzema ba zai buga gasar Kofin Duniya ba

0
107

Ɗan wasan gaba na Faransa kuma gwarzon ɗan ƙwallon duniya na bana, Karim Benzema, ba zai buga gasar Kofin Duniya da ake shirin farawa ba a yau a Qatar.

Benzema mai shekara 34 ya sake jin rauni a jiya Asabar yayin atasayen da tawagar Faransa ke yi jim kaɗan bayan ya murmure daga raunin da ya ji tun da farko.

“Raina ya ɓaci sosai game da Karim, wanda ya ɗauki gasar nan da muhimmanci sosai,” in ji kocin Faransa Didier Deschamps.

Shi kuwa Benzema bayyana alhininsa ya yi. “A rayuwata, ban taɓa sarewa ba amma a yau dole ne na jajanta wa tawagarmu kamar yadda na saba,” a cewarsa.

“Dalili shi ne dole ne na bar wa wani gurbina wanda zai taimaki tawagarmu buga wasa mai kyau a Kofin Duniya.