Trump ya ƙi yarda ya koma amfani da shafinsa na Tuwita

0
86

An sake bude shafin Tuwita na tsohon shugaban Amirka Donald Trump, bayan mai kamfanin Elon Musk, ya ce abar abokan hulda a shafin su bayyana ra’ayinsu kan ko ya bar Trump din ya ci gaba da amfani da shafin ko akasin hakan.

Mista Elan Musk ya ce sama da mutane miliyan 15 ne suka kada kuri’ar , kuma daga karshe masu son Trump ya dawo shafin sun rinjayi wadanda ba sa muradi.

Kusan kashi 52 cikin 100 sun kada kuri’ar marawa tsohon shugaban baya.

Sai dai a iya cewa Donald Trump ya badawa Tiwita kasa a ido, inda ya ce akai kasuwa, ba ya sha’awar sake komawa Tiwita.

Ya ce gara ya ci gaba da amfani da shafin sada zumunta na Truth na kashin kan sa, wanda ya kaddamar jim kadan bayan Tiwita ya toshe shafinsa da haramta ma sa amfani da shi a bara.

An dakatar da tsohon shugaban amfani da shafin na Tiwita a shekarar 2021, kan zargin tada zaune tsaye da tunzura magoya bayansa, da kai hari kan zauren majalisar Capitol ta Amirka bayan kin amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa da Joe Biden ya yi nasara.