Yajin aiki ya sa ni koyarwa kyauta a makarantar sakandaren garinmu

0
110

Yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU a Najeriya ya tilasta wa wani ɗailibin jami’a mai suna Muhammad Bala Garba koyarwa kyauta a ƙananan makarantun sakandiren unguwarsu har guda biyu.

Dalibin ya bayyana haka ne a yayin wata hira da BBC a shirin da muke yi na musamman game da abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a gabanin zaben kasarnan na 2023.

Muhammad, wanda ke ajin ƙarshe a Jami’ar Maiduguri inda yake karanta fannin nazarin kiwon lafiya (Health Education), ya ce ya rungumi koyarwa ne domin dama tuni ya saba da ita tun lokacin da yake koyon sanin makamar aiki a shekarar 2018, kuma tun a wancan lokacin ne ya saba da ɗaliban.

Kasancewar ƙungiyar ASUU tana yajin aiki sai ya ga ya kamata ya koma makaranta ya riƙa koya wa ɗalibai karatu kyauta.

Muhammad Bala Garba, wanda ke zaune a unguwar Hausari/Zango a birnin Maiduguri, ya ce yana koyarwa a makarantu guda biyu da suka haɗa da Mala Kachalla Model Junior Secondary School, da Mafoni Junior Day Secondary School, ko da yake daga baya ya ce ya daina koyarwa a makarantar Mafoni sakamakon wasu dalilai.

Ya kara da cewa a lokacin da aka tsunduma yajin aikin ASUU, akwai wasu makarantu masu zaman kansu guda uku da suka nemi da ya je ya riƙa koyarwa a can domin su riƙa biyansa, amma kuma sai ya ƙi saboda a cewarsa ya riga ya saba da waɗancan makarantu don haka ba zai iya tafiya wasu makarantun ya bar waɗancan ba.

Dalibin ya ce akwai wani abokinsa da ya taɓa ce masa me ya sa ba zai tafi makaratun da suke nemansa domin su biya shi kuɗi ba?

Sai shi kuma ya ce masa haƙiƙa ba zai iya tafiya domin kuwa su waɗancan makarantu ko ”ban je ba za su iya ɗaukar wani malamin ya je ya koyar domin su biya shi”.

Amma a ganinsa a waɗanan makarantun da ya saba idan ya daina zuwa wa zai zo ya koya wa ɗimbin ɗaliban da suka saba da shi.