Kwankwaso ya ziyarci gwamnan jihar Ribas don kaddamar da bude wasu aiyuka

0
59

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a daren Lahadi ya tarbi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, a Birnin Fatakwal, babban birnin jihar, gabanin kaddamar da titin Mgbutanwo da ke karamar hukumar Emohua a yau Litinin.

Wike ya gayyaci ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa bude ayyukansa daban-daban a Ribas, ya ce ya gayyaci ‘yan siyasa daga Jam’iyyun adawa don bude ayyuka a jiharsa domin su gani da idonsu su kuma shaida wa ’yan jam’iyyunsu.

Tsohon shugaban jam’iyyar (APC) na kasa, Adams Oshiomhole a ranar Larabar da ta gabata ya kaddamar da gadar sama ta 8 a jihar da ke kan titin Ada George, cikin karamar hukumar Obio-Akpor.

Shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kaddamar da gadar sama ta 9 a babbar mahadar Ikoku a ranar Alhamis.

Hakazalika, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da makarantar koyon aikin lauya ta Nijeriya a Fatakwal ranar Juma’a.