Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina a ranar Talata ya zubar da hawaye a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin gwamnatinsa a gaban majalisar dokokin jihar.
Kasafin kudin wanda ya kai Naira biliyan 288.63, an ware kashi 63.77 a matsayin babbar hanyar kashe kudi da kuma kashi 36.23 na ayyuka na yau da kullum.
A cewar Masari, an tsara kasafin ne domin kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma kaddamar da wasu manyan ayyuka da za a iya kammala su a cikin rayuwar gwamnatinsa.
Ayyukan sun karkata ne a sasshen Ilimi, Lafiya, Albarkatun Ruwa, Noma, Muhalli, Hanyoyi da Raya ababen more rayuwa.
Masari ya zubar da hawayen ne yayin da yake bayyana cewa kasafin kudin ya yi kadan ba kamar na shekarar 2022 wanda ya kai kusan Naira biliyan 34.