HomeLabaraiHadarin mota ya lakume rayuka 37 a Borno

Hadarin mota ya lakume rayuka 37 a Borno

Date:

Related stories

INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta...

IPOB ta umarci ‘yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB,...

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir...

Mata magoya bayan PDP na zanga-zangar kin amincewa da zabe a Kaduna

Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar...

Wani hadarin mota da ya auku a kan hanyar Maiduguri  zuwa Damaturu ya lakume rayukan mutane 37 a ranar Talata.

Babban jami’in Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC mai lura da shiyya ta 12, wadda ta kunshi jihohin Bauchi, da Borno da Yobe, ACM Rotimi Adeleye ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce motoci biyu ne kirar ‘Hummer’ ne suka yi taho-mu-gama da juna hadi da wata karamar mota kirar Golf, nan take kuma suka kama da wuta inda mutum 37 da ke cikin motocin suka mutu sakamakon konewa da suka yi.

“Mummunan hadarin ya afku a safiyar yau a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu kusa da wani kauye mai suna Jakana.

“Motocin Toyota bus samfurin Hummer guda biyu da salon golf daya ne suka ci karo da junan wadda  ya zuwa yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane 37 kuma yawancinsu sun kone ba a iya gane su ba,” inji shi.

“Bayan samun labarin aukuwar hadarin mun tura jami’anmu tare da na Hukumar Kashe Gobara domin aikin ceto.

“Kazalika, mun tuntubi Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Borno domin samun umarnin kotu na binne mutanen da suka kone ta yadda ba a iya ko gane kamanninsu.”

Jami’in ya kara da cewa, gudun wuce-kima ne ya haddasa aukuwar hadarin, inda ya yi kira ga direbobi da su kaurace wa dabi’ar gudun wuce-sa’a yayin tuki.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories