Cibiyar kula da makamai ta Najeriya zata lalata makamai 3,000 da aka kwato

0
101

Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ta hannun cibiyar kula da kananan makamai ta kasa (NCCSALW), ya bayyana shirin lalata kananan makamai sama da 3,000 na haramtattun makamai da sauran kayayyakin da aka kama a fadin Nijeriya.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa an yi kamen ne ta hanyar yaki da ‘yan ta’adda daban-daban a yankunan Arewa-maso-Yamma, Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da Arewa ta tsakiya na kasar nan cikin watanni 18 da suka gabata.

Da yake jawabi ga manema labarai gabanin shirin lalata makaman da za a yi a Kaduna a ranar Alhamis, Kodinetan Hukumar NCCSALW, Manjo Janar Abba Muhammed Dikko (rtd), ya bayyana cewa an mika makaman ne ga cibiyar daga hukumomin tsaro dake yaki da ‘yan ta’adda a sassan kasar nan daban-daban.

Ya ce hakan na cikin namijin kokarin da shugaba Buhari ke yi na magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.

Manjo Janar Abba ya kara da cewa, abinda yasa bai sanya Arewa maso gabas acikin yankunan da aka kwato makaman ba, sabida ‘yan ta’addan da dama sun mika wuya da makamansu wa gwamnatin jihar Borno a yankin.