Zabibi da bula da algarura: Ƴan Najeriya sun cashewa sabbin kudin naira

0
64

Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun naira da aka sauyawa fasali, ƴan ƙasar nan  suka yi wa batun ca ta hanyar bayyana ra’ayoyinsu kan hakan.

Shafukan sada zumunta na Facebook da Tuwita da Instagram da Tiktok da ma Whatsapp sun zama wuraren da ba a zancen komai sai na sabbin kudin.

Da yawan mutane sun nuna rashin jin dadinsu kan tsarin sabbin kuɗin, suna cewa ba su zaci haka sauyin zai zo ba.

An ƙaddamar da kuɗaɗen ne a wajen taron mako-mako da ake yi a fadar shugaban ƙasar a Abuja a ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar.

A shafukan Facebook da Tuwita, sai da ya zama shi ne babban batun da aka fi tattaunawa a kansa tun daga ranar Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis.

Tiktok ma ba a bar shi a baya ba, don yawanci matasa ƴan Najeriya da ke amfani da shafin sun mayar da hankali ne yin raha da barkwanci kan lamarin.

Yayin da Whatsapp da Instagram suka zama wajen da kusan kowa ya dinga wallafa sabbin kudin a sitatus (status) da sitori (story) ɗinsu.