DSS ta janye karar da ta shigar kan Tukur Mamu

0
134

Hukumar tsaron farin kaya, ta janye karar da ta shigar gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, na ci gaba da tsare tsohon mai sasantawa da ‘yan ta’adda, Tukur Mamu.

Lauyan DSS, A.M. Danlami, ya shaidawa mai shari’a Nkeonye Maha cewa hukumar ta janye bukatarta, jim kadan bayan da aka bukaci a saurari karar.

Rahotanni sun nuna cewa an shigar da karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1619/2022 tsakanin SSS da Tukur Mamu, domin ci gaba da shari’a kan jerin tuhume-tuhumen da ake masa.

Hukumar tsaro ta bakin lauyanta Ahmed Magaji, a ranar 13 ga watan Satumba, ta bukaci kotu ta ba da umarnin tsare Mamu na tsawon kwanaki 60 a matakin farko, har sai an kammala bincike. .

Kusan watanni shida bayan da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, sauran 23 da aka yi garkuwa da su a karshe sun sami ‘yanci a ranar 5 ga watan Oktoba bayan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ta yi.