Sai mun kawo kuri’un Kano ko da tsiya – Abdullahi Abbas

0
119

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, a ranar Laraba ya ce jam’iyyar su za ta yi nasara a zaben gwamnan ko da lalama ko da tsiya

Abbas ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wajen kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar a Gaya kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Ya ce, “Mutane na cewa in daina cewa APC za ta lashe zaben jihar Kano ‘ko da lalama ko da tsiya’. Ina so in shaida wa wannan taron cewa APC za ta lashe zaben jihar Kano ‘ko da lalama ko da tsiya’. A yau mun nuna kudurinmu na cin zabe tun daga sama har kasa a shekarar 2023.