Dan Allah a daina yi wa ƴan sanda mummunar fahimta – Sufeto janar

0
72

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bukaci ‘yan Najeriya da su sauya fahimtar su kan ‘yan sanda, domin inganta ayyukansu.

Alkali Baba, wanda kwamishinan ‘yan sanda Ade Hamzat ya wakilta, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a wani babban taron ‘yan sanda na yini daya mai taken: “Sabbin Manufofin Aikin Ɗan Sanda a Nijeriya.

Ofishin gyaran fuska da Ci gaban na ‘yan sanda, PORTO ne ya shirya taron tare da goyon bayan sauran abokan hulda da suka hada da Cleen Foundation da MacArthur Foundation.

IGP din ya ce akwai bukatar a sauya mummunar fahimta da jama’a ke yi wajen yin mu’amala ga ‘yan sanda a yayin gudanar da ayyukansu.

“Dole ne a samu ingantaccen sauyi na ra’ayin jama’a game da ‘yan sanda domin a samu daidaiton sauye-sauyen aikin ‘yan sanda a kasar,” in ji shi.

“Kamar yadda na fada, su ma ‘yan sanda a na cin zarafinsu.

“Lokacin da muka yi aikin ɗan sanda a da abokan aikin mu a wajen Najeriya kuma mu ka ga hadin kan da ‘yan sanda ke samu da ga jama’a, kuma muka kwatanta ayyukanmu a wajen Najeriya, sai mu ka gano cewa bambamcin aikin ɗan sanda a can da nan gida Nijeriya a bayyane ya ke.

“Saboda a Najeriya, kungiyoyin farar hula na goyon bayan jama’a, amma su wane ne suke goyon bayan ‘yan sanda saboda an tauye hakkinsu su mam,” in ji shi.