Jamus ta samu kwarin gwiwar ci gaba da kasancewa a gasar kofin duniya

0
123

Niclas Fullkrug ya bai wa Jamus kwallo mai mahimmanci da ta ba su canjaras  a wasan da suka fafata da Spain a jiya Lahadi a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar a yanzu haka.

Jamus sun samu haske a kokarinsu na tsallakawa zuwa zagaye na gaba a wannan gasa, sakamakon rashin nasarar da Japan suka yi a hannun Costa Rica tun da farko a jiya Lahadi.

Yaran na Hansi flick na bukatar doke Costa Rica a wasan karshe na rukunin E, kuma za su yi  fata Japan ba za su bai wa Spain mamaki ba a haduwar da za su yi.

Spain, sun samu kwallonsu na farko ne a minti na 62, bayan da Alvaro Morata, wanda ya shiga bayan hutun rabin lokaci ya yi amfaanni da kwallon da Jordi Alba ya kawo mai kamar yadda ya kamata.