Sarkin Musulmi ya buƙaci Miyetti Allah ta taimaka wa gwamnati kan matsalar tsaro

0
54

Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah da su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Yayin da yake magana a Abuja babban birnin ƙasar lokacin bikin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar, sarkin Musulmin ya ce al’ummar Fulani makiya masu son zaman lafiya ne.

Muhammad Sa’ad Abubakar III wanda shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci, ya yi kira ga sabbin shugabannin ƙungiyar da su yi ƙoƙarin taimaka wa gwamnati wajen magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.