Kotu ta daure mataimakiyar shugaban kasar Argentina

0
45

A ranar Talata wata kotun kasar Argentina ta yanke wa Mataimakiyar Shugaban Kasar Argentina, Cristina Fernández, hukuncin daurin shekara shida.

Hukuncin kotun ya kuma haramta wa Fernández rike mukamin gwamnati har karewar rayuwarta.

Kotu ta yanke mata wannan hukuncin ne bayan da ta same ta da lafin yin ruf da ciki kan Dala miliyan daya da aka ware don aiwatar da ayyukan gwamnati.

Sai dai kotun ta wanke Fernández daga zargin mallakar haramtaccen kamfani, wanda inda ya tabbata, hukuncinsa daurin shekara 12 ne a gidan yari.

Wannan shi ne karon farko da irin hakan ta faru a tarihin kasar ta Argentina.

Sai dai, wannan hukuncin ba zai tabbata ba har sai bayan Fernández’s ta daukaka kara, kuma ya zamana ba ta yi nasara ba.

Haka nan, ba zai yiwu a kama ta ba saboda rigar kariyar da take sanye da ita albarkacin mulki.

Tuni dai magoya bayan Fernández suka sha alwashin haifar da cikas ga harkokin kasar ta hanyar zanga-zanga.