Kwamitin Gudaji Kazaure haramtacce ne, ba Buhari bane ya kafa shi – Garba Shehu

0
63

A Najeriya, fadar shugaban kasar ta mayar da martani kan wani ikirari da kwamiti na musamman da shugaban kasar ya kafa domin ya gudunar da bincike a kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki.

Shugaban kwamitin, Gudaji Kazaure ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna kokarin hana ruwa gudu game da aikin nasa, da kuma hana shi ya mika wa shugaba Muhammadu Buhari rahotonsa.

A cewar kwamitin wanda aka dora masa alhakin binciken cajin kudin ajiya da cire kudin tun daga shekara ta 2013 zuwa yanzu, ya gano cewa babban bankin kasar ya tara fiye da naira tiriliyon tamanin, amma ya yi zargin cewa ana sama da fadi da kudin.

Malam Garba Shehu, shi ne mai magana da yawun shugaban kasar Najeriya ya yi karin bayanin kan wannan batun ga BBC.

“Wannan magana ta Gudaji Kazaure ba za a ce kwamiti ne ba. E, ya kafa kwamiti da kansa kuma ya nada jami’ai a ciki har da alkalin alkaln Najeriya da wasu mambobi. Ya sami shugaban kuma ya nuna masa kwato kudade na kasa za a yi.”

Garba Shehu ya ce duk mutumin da ya gaya wa Buhari cewa zai kwato kudi, zai ce masa Allah-san-barka, sai dai ya musanta cewa shugaban kasa ne ya kafa kwamitin:

“A zahirin gaskiya, duk wanda ya san yadda gwamnati ke tafiya, babu yadda za a ce shugaban kasa a bangaren gwamnati ya kafa kwamiti ya ba wa dan majalisa sakatare, ya kuma kira alkalin alkalai ya nada shi mamba. Ai an yi wa tsarin mulki karen tsaye.

Ya ce kwamiti haramtacce ne, “ba shi da hurumi a doka, shi yasa Shugaba Muhammadu Buhari yace a rusa shi, a kuma kafa sabo wanda ke karkashin ministan shari’a.”

Ya kuma bayyana mamakinsa kan yawan kudaden da Gudaji Kazaure ke ambatowa a kalamansa da ke cewa biliyoyin daloli ne aka yi badakkalarsu.

“Wannan zargi na tiriliyan 160 da yake cewa sun salwanta, ina kudin suke? Tiriliyan 160 fa.”

Ya ce idan aka tattara dukiyar da dukkan bankunan Najeriya wuri guda, ba su kai kashi daya cikin uku na kudaden ba.