Afrika na alfahari da tawagar kwallon kafa ta Morocco – Buhari

0
54

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya ‘yan wasan kasar Morocco da Atlas Lions da kuma sarkin kasar Sarki Mohammed VI murnar kafa tarihi a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a kasar Qatar.

A yayin da kasar ta samu tikitin zuwa wasan kusa da na karshe a kofin duniya.

Har ila yau, tawagar ita ce ta farko a Afirka da ta samu gurbin zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022.

A cewar Buhari, Maroko ta yi wa daukacin nahiyar alfahari da kwazonta, tare da ba da fata cewa lallai wata tawagar Afirka za ta iya yin nasara, kuma ya kamata ta lashe gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar.

Buhari ya yabawa kungiyar bisa kwarewa da aikin hadin gwiwa da suka yi, yana mai cewa ba za a iya cimma hakan ba sai da irin rawar da mahukuntan kasar Morocco suka taka wajen hada wata babbar tawaga.