Da zarar an kawo kwafin shari’ar Abduljabbar gabana zan rattaba hannu a zartar – Ganduje

0
63

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce takardun sa hannun hukuncin ya rataye Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Abduljabbar kawai yake jira. Inji Aminiya

Wata kotun musulunci ce da ke zamanta a Kano ta zartar da hukuncin kan zargin Malamin da batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka gurfanar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotun Kofar Kudu da ke birnin Kano.

Tun da farko Mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya ce ya gamsu da shaida da hujojjin da aka gabatar masa game da karar da ake yi wa Abduljabbar na yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

Ya ce hujojji sun bayyana cewar Abduljabbar ne ya kirkiro dukkanin wadannan kalamai a cikin karatunsa.

Don haka kotun ta same shi da laifin aikata aifin da ake tuhumarsa da shi wanda aka shafe watanni 15 ana shari’a.