Gwamnatin Jihar Ebonyi ta baiwa jami’an tsaro umurnin harbe duk wani bata garin da aka gani yana dauke da bindiga ko kuma wani makamin hallaka jama’a domin kawo karshen kashe kashen fararen hular da ake samu a jihar.
Rahotanni sun ce daukar wannan mataki ya biyo bayan tashin hankalin da aka gani jiya Litinin, inda wasu tsageru dauke da makamai da ake zargin magoya bayan haramcacciyar kungiyar IPOB ne, sun kutsa kai cikin birnin Abakaliki suna harbe harbe da rana, abinda ya razana mutanen garin wadanda suka rufe shaguna da kasuwanni da kuma bankuna.
Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kai harin Abakaliki ne da zummar tabbatar da umurnin hana zirga zirga na kwanaki 5 da shugaban wani sashe na kungiyar IPOB ya bayar.
Wannan hari yayi sanadiyar hallaka wasu mutane tare da jikkata wasu da dama, duk da yake kwamishinan yada labaran Jihar yace babu wanda ya rasa ransa sakamakon harbe harben.
Orji ya zargi maciya amanar jihar da yada labaran tilastawa mutane zaman gida da zummar razana su domin ganin basu gudanar da harkokin su na yau da kullum ba.
Kwamishinan ya ce Gwamna David Umahi ya kuma bai wa jami’an tsaron da ke aiki a jihar, tare da rundunar Ebubeagu umurnin ci gaba da sintiri a Birnin Abakaliki da kuma wasu biranen jihar domin tabbatar da tsaro.
Idan dai ba’a manta ba, Simon Ekpa, daya daga cikin shuganannin dake fafutukar kafa kasar Biafra, ya sanar da cewar za su kaddamar da shirin zaman gida na tilas na kwanaki 5 daga ranar 9 ga watan Disamba zuwa 14, a ci gaba da fafutukar ganin sun cimma muradunsu.