2023: Atiku ya bayar da Naira miliyan 50 ga wanda matsalar rashin tsaro ta shafa a Katsina

0
56

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga wadanda matsalar tsaro ta shafa a jihar Katsina.

Ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Katsina Dr Abdulmuminu Kabir Usman a fadarsa a wani bangare na yakin neman zabensa.

Atiku ya ce ya je fadar ne domin neman shawara da addu’a da albarka daga wajen mahaifinsa a yunkurinsa na zama shugaban kasar.

Ya ce ya damu da matsalolin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da ke damun sassan kasar nan, ya kuma yi alkawarin mayar da hankali a kansu idan aka zabe shi.

A martaninsa, Sarkin ya ce Da haske a yunkurin Atiku na zama shugaban Najeriya a 2023.
Sarkin ya ce ya ji dadin yadda dan takarar shugaban kasar ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da tattalin arziki, wadanda ya ce su ne batutuwan da suka kai shi asibiti kwanan nan.
Ya yi addu’ar Allah ya sa a yi zabe cikin nasara da kwanciyar hankali a 2023, inda ya ce kasar nan ta kowa ce ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba.
Atiku yana Katsina tare da mataimakinsa dan takarar shugaban kasa, Ifeanyi Okowa; Dan takarar Gwamnan Katsina, Sen. Yakubu Lado; da kuma babban daraktan yakin neman zabensa, Aminu Waziri Tambuwal.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da; tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; tsohon gwamnan Kano, Sen. Ibrahim Shekarau; tsohon gwamnan Kaduna, Sen. Ahmed Muhammad Makarfi; tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliy da kuma tsohon kakakin majalisar, Yakubu Dogara; da kakakin yakin neman zaben Dino Melaye da dai sauransu.
Tun daga fadar sarkin, jirgin yakin neman zaben ya koma gidan iyalan ‘Yar’aduwa domin yiwa Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa gaisuwar ban girma, sannan ta nufi filin wasa na Muhammadu Dikko Katsina, inda aka gudanar da gangamin yakin neman zaben.