Zamfara za ta dauki mayakan sa kai 2,000 don yaki da ‘yan bindiga

0
68

Gwamnatin Zamfara ta amince da daukar sabbin mayakan sa kai dubu 2 don shiga cikin rundunar yaki da ‘yan bindigar wadda gwamnatin jihar ke tafiyarwa a kokarin baiwa jama’a cikakkiyar kariya daga batagarin.

Shugaban kwamitin da ke kula da dakarun masu yaki da ‘yan bindigar a Zamfara Mr Bello Bakyasuwa a jawabinsa gaban manema labarai jiya Alhamis a birnin Gusau, ya ce sun karbi umarnin daga Gwaman Bello Matawalle game da daukar sabbin ‘yan sakan.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ne ya yi umarnin kafa kwamitin na musamman don yakar matsalolin ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi.

A cewar Bello Bakyasuwa akalla mutane dubu 6 da 700 suka mika takardun neman aikin a sassan jihar ciki har da mata said ai duka-duka mutum dubu 2 za a dauka don gudanar da aikin.