Mutane tara sun mutu a turmutsitsin sabuwar shekara a Uganda

0
61

Akalla mutane tara ne suka mutu sakamakon turmutsetseniya da aka samu a wata babbar  kasuwa, yayin gudanar da shagulgulan bikin sabuwar shekara a Uganda ranar Lahadi.

Bayan wasan wuta da aka yi a wajen babbar kasuwan Freedom City da ke Kampala, “an yi turmutsutsu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar nan take tare da jikkata wasu da dama,” in ji kakakin ‘yan sandan, Luke Owoyesigyire.

“Masu bayar da agajin gaggawa sun isa wurin inda suka kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar tara.”

Owoyesigyire ya ce “matasa” na cikin wadanda abin ya shafa, ba tare da bayar da karin bayani kan shekarun su ba.

Ya ce ayyukan “rash” da ” sakaci ” sun haifar da bala’i.

Bikin da aka yi maraba da shi a shekarar 2023 shi ne na farko a kasar da ke gabashin Afirka cikin shekaru uku, bayan takunkumin da ke da alaka da cutar ta Covid-19 da kuma batun tsaro.