An daure ‘yan majalisa biyu bayan sun daki wata ‘yar majalisa mai juna biyu

0
62

Wasu ‘yan majalisar kasar Senegal biyu za su shafe watanni shida a kurkuku bayan ta same su da laifin hambarar wata ‘yar majalisa mai juna biyu a ciki yayin da ake tafka muhawara a zauren majalisar kan kasafin kudin kasar.

‘Yan majalisar – wadanda dukansu maza ne – sun kai wa Amy Ndiaye hari ne bayan da ta soki wani shugaban addini kuma jagoran wata jam’iyyar siyasa na kasar.

Alkalin kotun da ta yanke wannan hukuncin ya kuma ci ‘yan majalisar biyu – Mamadou Niang and Massata Samb – su biya Uwargida Ndiaye CFA miliyan biyar (dala 8,100.00) domin cin mutuncinta da suka yi.

Harin da suka kai wa ‘yar majalisar ya janyo kakkausar suka a fadin kasar, kuma ya haifar da wata mahawara kan ‘yancin mata.

An kuma yada bidiyon harin a intanet, inda ake iya ganin Mista Samb yana tafiya zuwa wurin da Amy Ndiaye ke zaune kuma da isarsa wurin sai ya koda mata mari yayin da ake muhawara kan kasafin kudin kasar ranar 1 ga watan Disamba.

Ta mayar da martani ta hanyar jifarsa da kujera, sai dai a daidai wannan lokacin wani dan majalisar na daban ya hambare ta a ciki.

Rikici ya barke a zauren majalisar yayin da sauran mambobi suka yi kokarin kwantar da hankula.

Madam Ndiaye ‘yar majalisa ce ta gamayyar jam’iyyun Benno Bokk Yakaar mai mulkin kasar, kuma ta suma jim kadan ta suma, lamarin da yasa aka yi fargabar cikin nata ya zube.

Kuma bayan an sallame ta daga asibiti, Madam Ndiaye ta ci gaba da zama cikin wani mawuyancin hali, kamar yadda lauyanta Boubacar Cisse ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sannan, duk da bidiyon harin da ‘yan majalisar biyu suka kai kan matar, lauyoyinsu sun kafe cewa wadanda suke wakilta ba su aikata laifin da ake tuhumarsu da aikatawa ba.

Sun kuma bukaci kotun ta tabbatar cewa ‘yan majalisar na da kariya ta doka daga fuskantar hukunci.

Daya daga cikin lauyoyinsu mai suna Abdy Nar Ndiaye ya shaida wa AFP cewa, “Za su ci gaba da zama a kurkuku zuwa lokacin da za a saurari daukak karar da suka yi.