Sakandiren ‘yan matan da kusan duka ɗalibanta ke da ‘ya’ya

0
159

Wata makarantar sakandiren ‘yan mata a jihar Texas ta Amurka na ƙoƙarin sauya yadda ya kamata a kula da rayuwar ‘yan mata masu ciki tare da ‘ya’yayen da suka haifa.

Tun a farkon shekarar 2021 ne, Halen ke cin abinci fiye da yadda ta saba.

Matashiyar mai shekara 15 ba ta san dalilin da ya sa yanayin cin abincinta ya ƙaru ba.

”Shin hakan ba wata matsala”? kamar yadda ta tambayi ‘yar uwarta, wacce ta ba ta amsa da cewa ”ba wani abu ba ne, ai dama hakan na faruwa da mutane”.

To sai dai Yanayin saurin fushinta ya sauya, domin kuwa takan yi yawan faɗa da abokai da ‘yan uwa.

Sanna kuma al’adarta ta daina zuwa. Sai a ranar bikin zagayowar ranar haihuwarta ne ta fahimci cewa tana da juna-biyu. ”Sam ba haka ba ne” in ji Helen.

Nan take ƙawayenta suka ƙaurace mata, suna masu zarginta da amfanin da jun-biyun da take da shi domin ”samun samari” kuma baban jaririn da ke cikinta, wanda ɗan ajinsu ne ya daina yi mata magana.

”Ba na son yin faɗa da su”, in ji Helen

Daga ƙarshe ta yanke shawarar barin makarantar da take zuwa a lokacin da cikinta ya tsufa.

Daga waje, makarantar Linconln kamar sauran manyan makarantun Amurka an shuka fulawoyi, ga manayn motocin ɗaukar dalibai a jiye, ga kuma tutar Amurka iska na kaɗa ta.

To amma daga ciki, kuka da ɓaɓatun jarirai na daga cikin surutun ɗalibai da ake iya jin sautinsu.

A jikin katangar makarantar an manne fastocin da ke nuna yadda za a kula da goyon ciki tare da yadda za a kula da jarirai.

Kuma a cikin makarantar akwai wani ɗakin kula da jarirai.

Makarantar wacce ke garin Brownsville a jihar Texas na kan iyakar ƙasar da Mexico.

Kuma ɗaya ce daga cikin makarantun Amurka da ke koyar da ilimin rainon ciki da kula da jarirai musamman ga ‘yan mata.

Haihuwa a tsakankanin ‘yan mata a Amurka ya ragu a cikin shekara 30 da suka wuce,.

To amma abin ba haka yake ba a tsakanin ‘yan matan da ke zaune a kudanci da tsakiyar Amurka su a tsakaninsu ba komai ba ne saɓanin sauran al’ummar ƙasar.

‘Yan matan kudancin Amurka sun fi takwarorinsu na sauran sassan ƙasar samun juna-biyu.

Haka kuma masana sun yi gargaɗin cewar za a iya samun ƙaruwar ‘yan matan da ke ɗaukar ciki, sakamakon dokar haramta zubar da ciki da kotun ƙolin ƙasar ta yi

Kusan duka ɗaliban makarantar Lincoln – wacce ita kaɗai ce makarantar da ke koyar da ‘yan mata yadda za su kula da renon ciki tare da kula da jarirai tun shekarar 2005.

Kuma galibi shekarun ɗaliban makarantar sun kama ne daga 14 zuwa 19.

‘A yanzu dole na riƙa yin tunani a kan jaririya ta kamar yadda nake yi don kaina’

Abin da ya ja hankalin Helen ta koma zuwa makarantar Lincoln shi ne domin ta riƙa zuwa makaranta da ‘yarta, kamar yadda ta ce.

Yayin da take magana da BBC a tsakanin azuzuwan makarantar ɗauke da ‘yar tata mai suna Janine ‘yar wata takwas da haihuwa, ta ce ”a yanzu dole na riƙa yin tunani a kan ‘ya ta kamar yadda nake yi a kaina”

Helen da ɗanta ɗan wata takwas

A lokacin da BBC ta ziyarci makarantar ta Lincoln Park, an kai wasu ɗalibai bakwai ‘yan ƙasa da shekara 14, tare da wasu ɗaliban uku waɗanda dukkansu ke da ‘ya’ya.

Manhajar karatun makarantar daidai yake da na sauran makarantun da ke gundumar, kuma dole sai ɗalibai sun ci jarrabawar kammala makarantar kafin a ba su shaidar kammalawa.

Bambancin kawai shi ne yadda ake gudanar da tsarin makarantar.

Alal misala duka motocin ɗaukar ɗaliban makarantar na da mazaunan ƙananan motoci ga jariran ɗaliban.

Da safe akan bai wa ɗaliban tare da ‘ya’yansu abincin karyawa.

Sannan kuma ‘yayan nasu kan halarci makarantar renon yara kyauta.

Ɗalibai na da damar yin fashin zuwa aji domin kai ‘ya’yansu asibiti ko ganin likita.

A ajin da ake koyar da darasin kimiyya an tanadi wani ɗan ƙaramin ɗaki ga iyayen za su iya shiga domin shayar da ‘ya’yan nasu idan suna buƙata.

ɗakin rainon jariran

‘Na shiga damuwa a rayuwata’

Alexis, ita ma kamar Helen tana da shekara 15 ne a lokacin da ta fahimci cewa tana da juna-biyu, ta yi amfani da abun gwajin ciki daban-daban har guda uku, kuma duka sun nuna cewa tana ɗauke da ciki.

To amma duk da haka ba ta yadda ba, har sai da ta ga likitanta, wanda ya tabbatar mata da cewa tana ɗauke da ciki. ”Na shiga halin damuwa sosai a rayuwata”, in ji Alexis.

”Ban so na daina zuwa makarantarmu ba, saboda na san ba abu ne mai daɗi ba”

To amma a yanzu da ta koma zuwa makarantar Lincoln, a yanzu jaririnta ya kusa kai wa shekara guda.

A lokacin da wata ɗaliba mai tsohon ciki ke ƙoƙarin shigowa ajin, duka hankalin ɗaliban ya koma gareta a daidai lokacin da ta kusa yin tuntuɓe a ƙoƙarinta na shiga ajin.

Alexis ta riƙe hannunta domin taimaka mata zama a kan kujerar da ke kusa da ita, tana mai tsokanarta da cewa ”in shafa cikin naki?”

Kawar Alexis

Wasu alƙaluma da hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka ta fitar sun nuna cewa ‘yan mata 15 ne masu shekara 15 zuwa 19 daga cikin 1,000 suka haihu a shekarar 2020.

Alƙaluman ba su ƙunshi ‘yan mata ‘yan ƙasa da shekara 15 ba.

Duk da raguwar ‘yan matan da ke haihuwa da aka samu a Amurka, jihar Texas ta kasance daga cikin johohin ƙasar 10 da ke da yawan ‘yan matan da ke haihuwa.

A garin Brownsville – inda makarantar sakandiren ‘yan matan take – haihuwa a tsakankanin ‘yan mata ya ƙaru da kashi 12 cikin 100.

A jihar Texas dole ‘yan matan da ke ɗauke da juna-biyu su bi matakan kula da jariransu waɗanda ke da tsauri, ko su fuskanci hukuncin dokar zubar da ciki idan suka yanke shawarar zubar da cikin.

Ficewa daga jihar domin zuwa jihar da ta halasta zubar da ciki domin zubar da shi, ba abu ne mai sauƙi ga talakawa ba, musamman masu ƙarancin shekaru.