Man United na shirin yin wuf da Giroud don maye gurbin Ronaldo

0
154

Tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea, Olivier Giroud yana daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar Manchester United ke son daukowa a watan Janairu.

 

Kungiyar na son daukar dan wasan dan kasar Faransa wanda ya taimakawa kasar kaiwa wasan karshe na cin kofin duniya na FIFA a shekarar 2022 a Qatar.

 

A watan Yuni ne kwantiragin dan wasan na AC Milan zai kare kuma har yanzu kungiyar ta Italiyar ba ta sake masa tayin tsawaita kwantiraginsa ba.