NDLEA ta cafke mutane 977 kan badakalar haramtattun kwayoyi

0
66

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wasu mutane 977 da take zargi da ta’ammuli da safarar miyagun kwayoyi a jihohin Adamawa da Taraba da Gombe a shekarar 2022. Hukumar ta kama jimillar kilo 2,757 na tabar wiwi da sauran magungunan asibitin masu tabin hankali cikin shekarar da ta gabata.

Idris Mohammed Bello, kwamandan shiyyar da ke kula da jihohin Uku na Adamawa da Taraba da Gombe ne ya fitar da wannan kididdigar a ranar Talata a hedikwatar shiyyar da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Bello, ya kara da cewa, daga cikin mutane 977 da aka kama, an yanke wa 365 hukunci, yayin da 374 ke karbar nasihohin gyaran hali.

Rahoton hukumar na shiyyar a shekarar 2022 ya nuna cewa, Hukumar ta kama kilo 1,808 na tabar wiwi da kuma kilo 949 na magungunan asibitin masu tabin hankali (kilo 2,757 ) daga wadanda ake zargin a jihohin uku a shekarar da ta gabata.

A cewarsa, mafi yawan mutanen 457 sun fito ne daga jihar Adamawa yayin da aka kama 290 daga Taraba sai 230 daga Gombe.