Ba zan kai ‘ya’yana karatu waje ba idan na zama gwamnan Kano – Abba gida-gida

0
58

Dan takarar Gwamnan jihar Kano a jam’iyyarmu NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya ce ba zai kai ‘ya’yansa kasashen waje yin karatu ba idan ya zama gwamnan jihar.

Abba, ya bayyana haka ne cikin wata tattauna wa da aka yi da shi ta shafin Facebook tare da mawallafin Jaridar ‘Daily Nigerian’, Jaafar Jaafar da Nasiru Salisu Zango na gidan rediyon Freedom da lauyan nan mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Bulama Bukari da kuma lauya Abba Hikima shi ma daga Jihar Kano.

Dan takarar ya kara da cewa yanzu haka ma yaransa guda biyu suna karatu ne a makarantun cikin gida mallakin gwamnatin Jihar Kano, wato jami’ar Yusuf Maitama Sule da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil.

Ya ce “An tabarbara harkokin ilimi saboda yaransu (‘yan siyasa) ba sa cikin makarantun ne ya sa duk basu damu ba”

A cewarsa, “Duk ‘ya’yan talakawa ne a cikin makarantun cikin gida kuma basu san wahalar da yaran suke sha ba,” in ji shi.

An sha sukar ‘yan siyasa da dama kan daukar yaransu zuwa kasashen waje don yin karatu.

Lamarin da ya sanya mutane ke ganin haka ne ya sa harkar ilimi ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan.

A watan Maris ne dan takarar na NNPP, zai kara da mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda shi ne dan takarar gwamna na APC da kuma Mohammed Abacha daga PDP da sauransu a zaben gwamnan jihar.