Illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi

0
168

Ina ganin haka ce ta sa tun shekaru aru-aru, ina digirgire in hau katako, ko teburi, in kunna Rediyon mahaifiyarmu (rahamar Allah ya je mata) da sauran al`ummar Annabi, nake jin wata waka ta wani mawaki mai suna BIBIYO KONKO a wakarsa da yake cewa “don Allah samari ku daina shan kwaya don shan kwaya masifa ce, takan sa mutum ya lalace!” Haka ma akwai wani mawakin Tangale mai suna LAMBALA a wakarsa da yake cewa, “Shan wiwi da kwaya sun dauka gayu ne!.

Koda yake zai wuya a ce wadanan fasihan mawaka na suna raye, amma dai sun nuna basira da kishin tarbiyar matasa, duk da yake wasu ba su ji rokon Bibiya Koko ba, kuma wasu matasan sun dauka gayu ne to ba gayu ba ne, gidadanci ne ba zan ce kauyanci ba, domin an ce duk asalin birini daga kauye ya fara kuma ba, a raina kauye, ko ko binni domin ko ba komai albarkatun gona na abinci ma fi yawa daga nan yake.

Mu dawo kan maganar illar ta`amali da miyagun kwayoyi ko shansu, ko dillancinsu sun yi kama da makamun kare dangi in wani mai karatu ko wani masani ya ce sun fI hatsari kan makamin kari dangi, ba zan mai musu ba. Saboda yana da hujja, idan ana maganar kare dangi dole a ba da misali da abin da ya faru a 1945 a Japan a harin antomic bom,na Hiroshima da Nagasaki, wanda aka ce fadawarsa ke da wuya ya kashe mutum 80,000 daga baya tiririnsa kuma ya kara kashe mutum fiye da dubu 10 suka kwanta dama.

Ka ga makamin kare dangi na da mumunar illa, amma ta`amali da miyagun kwayoyi ya yi kama da makamun kare dangi domun al`ummar da take sha, ko ta`amali da miyagun kwayoyi ko dillacinsu, to duka ba mai kai labari ko da kowa da ransu, za su ga mumunan karshe.

Mumunan sakamako kuma, ko suna raye to suna mace ne, kamar yadda bom ke kashe muta ne, domun rayuwa ce mara amfani tako wace fuska, dan haka akwai ila da illoli ga wannan dabi`a da Nijeriya, take da hukuma kusum da guda ta NDLEA ta yaki da wannan dabi`a da muka zayana kuma ba shaka kowa ya san wannan hukuma

Kafunmu shiga magana a Nijeriya, kai tsaye bari mu kali irin illolin da ta`amali da shan miyagun kwayoyi da dillancinsu, ya yi wa siyasar duniya kaca-kaca dubi kasar Kwalambiya, wanda dilalan mugan kwayoyi ne ke juya kasar, wannan ne ma ta sa ake ganin kasa Kwalambiya, na daya daga cikin sansanin mugan dilllan kwayoyi na duniya in har bayanai da bincike ya tabbata akan abun da ake bayana kasar Kwalambiya, haka ne, ga kasar Makziko, na daga cikin kasashen da ake zargi da irin wadanan abubuwa marasa dadi, domun in ba manta ba.

Labari da ya fito ma fi karfi daga makziko a ranar karshe ta tsohuwar shekara ta 2022 shi ne wasu da ake zargi da ta ammali da mugan kwayoyi sun fasa gidan kurkuku ko gidan kaso, ‘yan uwansu masu yawa sun arce, ka ga wannan ya nuna Barazana ga duka da oda aduk inda mashaya ko dilalan kwaya sukayi yawa inba duka da oda akwai matsala a rayuwa, da barazanar zaman lafiya, haka an rawaito a kasar Senigal wasu ‘yan majalisa biyu alkali ya yanke musu hukuncin wata shida a gidan gyaran hali da biyan tarar saifa milliyan biyar kan mangare wata mata yar majalisa a majalisar kasar, any aba kwaya suka sha ba.

A Nijeriya, bayanai sun nuna cewa hukumar NDLA ta kama mashaya ko masu ta`amali da mugan kwayoyi sama da dubu 18 a shakara biyu rak wanda za ka kira wannan nasara ce ga al`umar kasa ba ga hukumar ba kadai domun ko a ranar 25 ga watan daya gabata anzargi wani jami`in tsaro da kashe wata lauya mai juna biyu any aba kwaya ba ya sha ba. Wasu yan uwan majinyata sun kaashe likita a jihar Dalta kan zargin litan da mutuwar dan`uwansu duk dai a wannan lokaci zai wahala a aikata mumunan laifi ba a sha kwaya ba.

Idan ka dawo kano labari mai faranta rai shi ne cewa kano da ake ganin na kan gaba wajen shan miyagun kwayoyi yanzu abun na raguwa sosai a kano na samun cigaba wajen raguwar wannan dabia kamar yadda wadanda su kai buncike a farko na cewa wai kano na ga ba, kuma su ne suka tabbatar da cewa kano na cigaba wajen samun nasarar da dakile sha da ta`amali da miyagun kwayoyi, musamam in aka yi la`akari da cewa a baya can akwai bayanai na masana wannan harkar cewa akwai kimanin muta ne miyan biyu da ake zargi da sha da miyagun kwayoyi a kano, sun ce Kenan duk cikin mutum shida akwai mutum daya mai shan kwayar da ba likita ne ya rubuta masa b,amma dai Kano ana kokari mutuka na dakile shan miyagun kwayoyi da ta ammali da su kamar yadda hukumomin jahar ke bayanawa a koda yaushe.

Illar shan miyagun kwayoyi sun taba ko ina na rayuwar dan`adam tun daga kan lafiyarsa da tunaninsa domun kowa ya san akwai wata halita a kwakwalwa da ake kira MEDULLA OBLONGATA kamar yadda na fahince ta a daya daga cikin darusan da muka yi na Biology kuma nassan dole tanada alaka da wani bayani duk dai a darsun sanin halitun da ake cewa da ke aikin kwakwalwa ne ake samun samun wata Jimla ta turanci Hearing And Interpretation of Speech ma`ana ita ce mai ji da fahimtar abu da kuma bayana shi na dan`adam, idan kuma ban fahimci haka ba, to masana ko likitoci sa gyara wannan kuskuran inda shi.

In kuma haka ne dama shi dan’jarida kullum na tare da masana iri-iri da sauransu da ake zanta wa da su dan ilimantar da kanasa da sauran mutane a kan fannoni daban-daban to tunda shan kwaya likitoci sun tabbatar yana gurbata tunani to ashe ko sham miyagun kwayoyi na da ban ban hatsari ga lafiyar dan`adam.

Illar shan miyagon kwayoyi ga tattalin arziki wanda kwaya ta bugar ba zai taimaki kansa ba, ba zai taimaki al`umar sa ba, ba zai taimaki kasar sa ba, aikuwa akwai ila babba,a ta`ammali ko sha miyagun kwayoyi a rayuwar dan`adam domin ba za asa wanda kwaya ta bugar ba shugabanci ba, na siyasa ko na addini ba, duk wani abu na yabu da ake san ci gaba masu shan miyagun kwayoyi indai gaskiya ne ba za su zama masu jagorantar abun kirki ba.

Wani masanin tahiri da siyasar duniya ya ce duk wata kasa ko wata daula da ake san ruguza ta daga nagarta da kyakyawan shugabanci zuwa lalacewa ta rashin bun doka da oda to a yake ta da cusawa matasanta shan miyagun kwayoyi shi ke nan ankarya ta ammata illa fiye da da illar da Atomic Bom ya yiwa Japan kimanin shekaru 78 da suka wuce domin duk da illar duk da aka jefawa Japan a yakin duniya na biyu japan dai yanzu na daga cikin kasashe masu ci gaban kimiyya da fasaha a duniya ashe kuwa shan miyagun kwayoyi ko ta’ammali da su ya yi kama da makamun kare dangi koma ya fi illa.

Akwai dai hanyoyi da masana daban-daban suka zaiyana wajen dakile wannan matsala a kowace jiha ko koma a ko wace kasa da ta samu kanta a wannan annoba ko bala`i ma fi muni wajen ruguza al`umma a addininta da iliminta da al`adunta da siyasar ta da tsaronta shi ne daukar mataki na kame dillalan miyagon gwayoyi da gurfanar da su gaban shari`a da yi musu hukunci dai dai da abun sukayi na amfani da mugun makami a kan al`uma na dabiar sha ko dillancin mugan kwayoyi su kuma wadanda aka kama da sha abun da ya kamata amusu a tsaresu a zaunar da su a sasu a layi na daina sha da kuma nuna musu illar shan mai makwan mashaya su zama masu amfani a kasar su da al`umarsu da dai sauran hanyoyi wanda hukumomin haki da sha da ta’ammali da dilancin mugan kwayoyi suka sani kuma suke kokari a kai sai dai kawai a yi abun da yake akan doka ba sani ba sabo domun babu wanda ya fi karfin doka ta hukunta shi sai mutum biyu wanda bai karya ta ba, sai kuma mai tabin hankali Allah shi kiyaye, ya ba mu lafiya ya raba al`umma da shan miyagun kwayoyi da ta’ammali da su.