Harin ‘yan ta’adda ba zai dakatar da sufurin jirgin kasa ba – NRC

0
129

Hukumar lura da zirga-zirgar jiragen kasat ta Najeriya ta ce harin da aka kai tashar jirgi na Ekehen da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo ba zai shafi aikin jirgin kasa na Itapkpe-Warri ba.

Manajan Darakta na Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya (NRC), Engr. Fidet Okhiria, wanda ya shaidawa manema labarai hakan, ya ce za a ci gaba da gudanar da aikin layin dogon, amma za a tsaurara matakan tsaro.

A ranar Asabar ne ‘yan bindiga suka kai harin tashar jiragen kasan tare da yin awun gaba da fasinjoji da ba a san adadin su ba, yayin da suke kokarin tafiya Warri.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Chidi Nwabuzor, wasu daga cikin fasinjojin sun samu raunuku saboda harbin bindiga.

Harin na baya-bayan nan dai ya zo ne kimanin watanni tara bayan wani hari da aka kai a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna inda aka yi garkuwa da fasinjoji da dama, lamarin da ya kai ga dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a yankin.

A ranar 5 ga watan Disamba, 2022 ne gwamnatin kasar ta bude hanyar layin dogon, bayan an sako sauran fasinjojin da aka yi garkuwa da su.