Kananan yara fiye da miliyan 5 ne suka mutu a 2021- Majalisar dinkin duniya

0
122

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana yadda kanana yara akalla miliyan biyar ’yan shekara biyar zuwa kasa suka rasa rayukansu cikin shekarar 2021, kari kan matasa ‘yan shekaru biyar zuwa 24 su kimanin miliyan daya da dubu dari da suka mutu duk dai a shekarar.

Gamayyar kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da ke tattara alkaluman mace-macen yara UNIGME cikin mabanbantan rahoton da suka fitar cikin makon nan, sun bayyana cewa yaro guda na mutuwa a duk dakika hudu da digo hudu wanda ke nuna asarar asarar yara fiye da miliyan biyar cikin shekarar 2021 duk da cewa shekarar ta kasance mafi karancin asarar rayukan jarirai da aka gani tun bayan shekarar 2000.

A cewar gamayyar rahoton a tsakanin lokacin da yaran fiye da miliyan biyar da kuma matasa miliyan daya da dubu dari daya suka mutu cikin shekarar ta 2021 an kuma haifi jarirai akalla miliyan daya da dubu dari tara kuma galibinsu sun samu kulawar da ta basu damar tsallake yawaitar mace-macen sabbin haihuwar da ake samu.

Kungiyoyin sun bayyana cewa matakan da gwamnatoci suka dauka na bunkasa bangarorin lafiya kama daga sashen haihuwa da kuma kula da sabbin haihuwar baya ga yaran da suka fara tasawa ya taimaka matuka wajen rasa asarar rayukan matasa daga haihuwa zuwa shekaru 24 a duniya.

Daraktan tattara bayanai na UNICEF, Vidhya Ganesh ta bayyana cewa, wajibi ne gwamnatoci su zage damtse wajen bunkasa bangarorin lafiya don dakile rasa rayukan babu gaira babu dalili musamman ga yara sabbin haihuwa zuwa shekaru biyar.

A cewar Vidhya Ganesh, mace-macen kananan yara ya ragu da akalla kashi 50 karon farko cikin wannan karni inda mace-macen matasa ya ragu da kashi 36 yayin da mace-macen sabbin haihuwa shi kuma ya ragu da kashi 35.

Sai dai Dakta Anshu Banerjee daraktan sashen kula da mace-macen sabbin haihuwa da matasa na WHO, ya bayyana cewa duk da wannan kankanuwar nasarar, wajibi ne gwamnatoci su mike tsaye wajen bunkasa bangarorin lafiya daidai lokacin da alkaluma ke nuna yiwuwar rasa rayukan kananan yara da matasa miliyan 56 nan da sekarar 2030 kari kan sabbin haihuwa miliyan 16 da za su iya mutuwa kafin wannan lokaci.