NIS ta kaddamar da cibiyar bayar da sabon ingantaccen fasfo a Kano

0
60

Babban shugaban Hukumar kula da shiga da fita ta ƙasa Isah Jere Idris, MFR, ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, ana samun ci gaba a shirin sauya fasalin fasfo da ake yi a halin yanzu, musannam kan tsarin yadda za a yi saurin gane waɗanda suka shigo daga sassa daban-daban na duniya.

Shugaban ya ce, yanzu haka a Kano, sun ƙaddamar da cibiyar aikin yin e-Passport da aka inganta na zamani, kuma suna ci gaba da faɗaɗawa zuwa sauran wurare.
Wanda ya wakilce shi a wajen taron, ACG Sadat Hassan, ya ce, ya yi matuƙar farin ciki da jin irin ci gaban da ake samu a dukkan sassan yin fasfo ɗin a dukkan faɗin ƙasar nan, wanda ya nuna yadda mutanenmu ke bayar da cikakken haɗin kai. “Mun shirya za mu shafe mako biyu cif muna yin wannan aikin daga yanzu har zuwa ranar 21 ga wannan watan na Janairu, wanda kuma a wannan lokacin ne za kamala shirin.”

Ya kuma ƙara da cewa NIS za ta ci gaba da bayar da fasfo ɗin a tsakanin mako uku zuwa mako shida, kana iya tura bayananka, musamman ga mutanen da ba su da matsala wajen tura bayanan ko kuma a rubuta takardar buƙata.Ya ƙara faɗa da babbar murya cewa NIN na daga cikin shika-shikan yin fasfo wanda kuma dole a tabbatar da cewa, bayanan da ke cikinsu ba su saɓa ba.

“Muna ƙara samun ci gaba ne don haka muke kira ga masu neman fasfo ɗin su guji yin bayanan ƙarya su tabbatar sun yi bayanan da kansu kuma sun biya dukkan kuɗaɗen da hannunsu , za su shigar da bayanansu ta hanyar shiga wannan adireshi, passport.immigration.goɓ.ng.Za kuma mu ci gaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen dukkan matsalolin da za a ci karo da su.”

Haka kuma ya ce, zai yi amfani da wannan damar wajen gode wa jama’a kan cikakken goyon bayan da suke samu a wajensu. Haka kuma ya nuna cewa, yanzu haka dai NIS ba ta ɗaukar mutane, kuma duk lokacin da za ta ɗauka za ta sanar a kafafe yaɗa labarai, wato lokacin da muka samu amincewar gwamnatin tarayya.