‘Yan bindiga sun kashe mutane 2 tare da yin garkuwa da matan aure 4 a Kaduna

0
117

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban al’umma kuma dan kungiyar agajin gaggawa ta Fityanul Islam tare da dan dan uwansa a gidansa da ke kauyen Unguwar Mai Awo a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

A harin, ‘yan bindigar sun yi ta harbe-harbe, sannan kuma suka yi awon gaba da wasu matan aure hudu ciki har da wata mai shayarwa a unguwar da ke kusa da fitaccen garin Jos da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da sanyin safiyar Laraba, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin furgici da rudani.