‘Yan bindiga sun sace DPO a jihar Filato

0
103

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace DPO din ‘yansanda a yankin Pankshin a jihar Filato.

LEADERSHIP, ta ruwaito cewa, DPO din wanda ba ambaci sunansa ba, an yi garkuwar da shi ne a wata karamar hukumar a ranar Alhamis.

Wata majiya kusa da ‘yansandan jihar ta ce, DPO din bai jima da fara aiki a matsayin DPO ba.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton kakakin rundunar ‘yansandan jihar Alfred Alabo, bai fitar da wata sanarwar a kan sace DPO din ba, amma bayan da aka kira shi ya ce, yana halartar wani taro ne.