Ronaldo da Messi za su hadu a wasa tsakanin Al Nassr da PSG

0
111

Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo zai jagoraci tawagar Al Nassr ta Saudi Arabia a matsayin kaftin yayin wasan sada zumuntar da kungiyar za ta kara da PSG ta Faransa a ranar Alhamis.

Wannan dai shi ne wasa na farko da Ronaldo zai buga tun bayan komawarsa Al-Nassr a watan da ya gabata a yarjejeniyar da zai rika karbar fiye da yuro miliyan 200 a shekara, kuma tuni aka dorawa Ronaldo alhakin jagorantar kungiyar da ke dauke da ‘yan wasa daga kungiyar Al-Nassr da Al-Hilal.

Ronaldo wanda inkiyar sa ita ce CR7, wannan ne karon farko da zai hadu da tsohon abokin dabinsa wato Lionel Messi, wanda ake ganin watakila ta kuma iya zama haduwarsu ta karshe lura da yadda suke kwallo a mabanbantan nahiyoyi.

Ronaldo da Messi na sahun ‘yan wasa biyu da suka yi dabi mafi kayatarwa a tarihin kwallon kafa ta yadda suka zama gangarau tare da mamaye fagen na tsawon fiye da shekaru 10 ta yadda suka lashe kyautar Ballon d’Or har sau 12 a tsakaninsu.

Yayin taka ledarsu a kungiyoyin Real Madrid da Barcelona da ke Spain, Ronaldo da Messi sun mayar da haduwar El-Classico mafi kayatarwa, gabanin Ronaldo ya bar Spain zuwa Juventus ta Italiya a shekara ta 2018.

Rabon da Gwarazan biyu su hadu da juna tun watan Disamba 2020 lokacin da Juventus ta yi tattaki zuwa Nou Camp.

Idan har Messi ya zabi tsawaita kwantiraginsa da PSG a wannan kakar, da alama ba zai kara fuskantar Ronaldo ba, ko da ya ke rahotanni sun ce Messi na da tayi mai tsoka a kan teburi daga Al-Hilal da Al Itihad da ke Saudiyyan lamarin da zai iya dawo da dabin zakarun biyu a gabas ta tsakiya.