Gwamnatin tarayya tayi magana kan tallafin man fetur [Ku karanta]

0
136
Man Fetur
Man Fetur

Akwai yiwuwar gwamnatin tarayyar Najeriya ta soma cire tallafin man fetur daga Afrilun 2023, wato watanni uku kafin yadda ainahin lokacin da aka yi niyyar cire tallafin a baya.

Ministar kuɗi da kasafi Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wata hira ta musamman da ta yi da gidan talabijin na Arise a yayin wani taro na tattalin arzikin duniya a Switzerland.

“Abin da ya fi shi ne wannan gwamnatin watakila ta soma cire tallafi a farkon zango na biyu na wannan shekara saboda zai fi nagarta idan aka cire a hankali a maimakon a jira a cire shi baki ɗaya,” in ji ministar.

Ta bayyana cewa duka ƴan takarar shugaban ƙasar Najeriya a lokutan yaƙin neman zaɓensu duk suna da ra’ayin cire wannan tallafin.

Bayan ƙara wa’adin watanni 18, gwamnatin tarayya ta shirya kashe naira tiriliyan 3.35 kan tallafin mai daga Janairu zuwa Yunin 2023.

Wannan ƙarin wa’adin da aka yi ya janyo muhawara matuƙa kan irin kuɗin da za a kashe sakamakon ana ganin cewa zai ƙara giɓi a kasafin kuɗi wanda kuma ana ganin idan aka samu giɓin sai an ranto kuɗaɗe.

Bankin duniya da Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF duk sun bayyana cewa cire tallafin man fetur na ɗaya daga cikin ginshiƙan da za su ɗaga Najeriya domin ta samu ci gaba.

An kusan shafe shekara guda ana cikin wahalar man fetur a Najeriya.

An soma wahalar fetur ɗin dai makonni kaɗan bayan an soma yaƙin Ukraine.

Dillalan man fetur dai a ƙasar a kullum na dora laifin kan gwamnati inda suke cewa suna bin basussuka kuma babu isashen mai.

Sakamakon wahalar man fetur ɗin ana sayar da man kan farashin da ya kai har 360 a wasu gidajen mai da ke faɗin ƙasar.

A kullum gwamnatin Najeriyar na cewa za ta kawo ƙarshen matsalar wahalar fetur ɗin amma abin ya ci tura.

BBC Hausa

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here