Rashin kishin ƙasa ne ke sa janye takara a yanzu – Kwankwaso

0
105

Dan takarar Shugabancin Najeriya a jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce idan ya samu nasara a zaben da ke tafe, ya kafa gwamnati, za su bai wa harkar tsaro muhimmanci gaske, inda za su kara yawan jami’ai da sojoji, wadanda za su karfafa tsaro a iyakoki na tudu da na ruwa da dazuka da kusan ko’ina a kasar.

Rabi’u Kwankwason ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a jiya, Laraba a Chatham House da ke birnin London game da manyan zabukan Najeriya na shekaran nan.

Dan takarar ya bayyana manufofinsa game da yadda ya fi dacewa a tafiyar da gwamnati da kuma sabbin matakan ya kamata a dauka wajen magance matsalolin kasa.

To bayan tashi daga taron dan takarar na NNPP ya shiga ofishinmu na London inda ya yi wa BBC karin bayani kan jawabin da ya yi a cibiyar.

“Mun je mun yi magana, kuma mun yi jawabi kan batutuwa masu dama, sannan abubuwan da karancin lokaci bai bari mun sanar da su ba, mun gaya musu muna da kundi da muka rubuta da ya kunshi manufofin jam’iyyarmu ta NNPP. Mun duba matsaloli, mun kuma kawo magungunan matsalolin da zarar mun sami kafa gwamnati.”

Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana wasu muhimman abubuwan da ya bayyana wa al’ummar Najeriya cikin jawanin nasa, sai dai ya koka da karancin lokacin da aka ware wa tawagarsa.

“Abubuawan da muka so fadi suna da yawa, amma duka taron ma gaba yanasa sa’a guda ne. Ni, an bani minti 20 ne domin in yi magana.”

Ya kuma ce ya yi tsakura ne cikin muhimman batutuwa, “Mun fara da maganar tsaro, domion na san wani abu kan tsaro – ganin cewa na yi ministan tsaro a karkashin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Obasanjo, inda na ba shi shwarwari kan matakan da suka dace a dauka domin kawar da matsalar ta tsaro.”

Ya ce karkashin tsarinsa, za a ninka yawan sojojin kasar, har sia an sami isassunsu wadanda za su kare doron kasa da gabar tekun da duka dazuzzukan kasa mai fadin dubban kilomitoci kamar Najeriya.

Kan shirin tunkarar babban zabe da ke tafe a watan Fabrairu da na Maris, Rabiu Kwankwaso ya ce tuni jam’iyyarsa ta NNPP ta shirya wa zaben.

“Yan Najeriya na farin ciki, domin talaka a halin yanzu ba ya bukatar mai ba shi naira dubu daya ko dubu biyu a ranar zabe ne ba, a’a suna neman ina ne mafita, ina ne za su zauna lafiya. Ina ne ‘ya’yansu za su tafi karatu a cikin kwanciyar hankali?”

Ya bayyana cewa a kokarinsa na mika sakon da jam’iyyar tasa ke da shi, ya yi tattaki zuwa daruruwan kananan hukumonin Najeriya:

“Yau naje kananan hukumomi 400 a Najeriya, a kafa. A shiga ta nan, a fita ta nan. A shiga ta nan, a fita ta nan.”

Da aka tambaye shi ko akwai kanshin gaskiya a ikirarin da wasu ke yi cewa akwai wani matakin da za a kai da zai sa ya janye daga takarar neman mukamin shugaban Najeriya, sai ya ce:

“Ai duk abin da za a fada an riga an fada, wannan magana ce ta makiya. A yanzu ma babu wanda zai janye wa wani. Ina da dan takarar mukamin gwamna 28 cikin jihohi 28 da za a yi zabuka. Ina da ‘yan takarar sanata 108 cikin ‘yan takarar kujeru 109 na majalisar dattawan Najeriya – dayan ma muna shari’a da hukumar zabe ta INEC kan batun.”

Ya kara da cewa jam’iyyarsa na da dukkan ‘yan takara a dukkan matakai har zuwa na ‘yan majalisar jiha, “A yanzu muna shirin tura wakilanmu na zabe daruruwa da dubbai. Ni a sanina babu wata jam’iyyar da ke da wakilai ko ejen-ejen kamar namu.”

Ya karkare jawabin nasa da cewa babu dalilin da zai sa ya bar wannan takarar, domin yin haka tamkar yin watsi da alkawurarn da yayi ne na taimakawa a gyara kasa, ya kuma ce “Ina kishin Najeriyar, ina dukkan abubuwan da muke ta fada?”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here