Rundunar ‘yan sanda ta ba wa iyalan jami’anta da suka mutu da wadanda suka jikkata biliyan 13

0
160

Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ta gabatar da cakin kudi na naira biliyan 13 ga iyalan jami’an ‘yan sandan da suka mutu da wadanda suka jikkata a bakin aiki.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Baba, ya gabatar da cak din ga iyalan jami’an ‘yan sandan da aka kashe tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.

IGP ya ce kimanin iyalai 6,184 na ma’aikatanta da aka kashe da wadanda suka jikkata za su ci gajiyar kudin.

IGP din ya kuma ce cak din ya shafi inshorar ma’aikatan, wadanda suka samu raunuka yayin da suke gudanar da ayyukansu.