An sace basarake mai daraja ta daya a jihar Filato

0
103

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da Sarkin kabilar Izere da ke karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato, Rabaran Isaac Wakili.

Wakilin LEADERSHIP ya rawaito cewa Sarkin mai daraja ta daya, an yi garkuwa da shi a fadarsa da ke gundumar Shere da misalin karfe 3 na safiyar ranar Juma’a zuwa wani wajen da ba a sani ba.

Shugaban karamar hukumar Jos ta Gabas, Ezekiel Izang, ya tabbatar da faruwar lamarin ga ‘yan jarida ta wayar tarho, inda ya ce, ‘yan bindigar sun mamaye garin tare da yin harbe-harbe kafin su samu shiga cikin fadar Sarkin su sace shi.

Wani ganau da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce, a yayin harin an harbi wani dan sanda da ke aikin tsaro a gidan Sarkin, sun kuma kashe wani jami’in tsaron sa kai da ke aiki a fadar yayin da ‘Yan bindigar ke kokarin sace Sarkin.

Har zuwa lokacin aiko da labarin nan ba mu samu jin ta bakin Kakakin hukumar ‘yansandan jihar, DSP Alfred Alabo ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here